Bankin na AFDB ya ce,idan aikin ya kammala, zai taimaka wajen bunkasa manufar kasar Kenya ta kara fadada hanyoyinta na samar da wutan lantarki a kasar.
Babban darektan ofishin banki mai kula da harkokin kasuwanci da raya yankunan gabashin Afirka, Gabriel Negatu ya ce, aikin zai kuma samar da guraben ayyukan yi da hanyoyin kudaden shiga, musamman ma ga mata.
A nasa bangaren shugaban kamfanin samar da wutan lantarki mai kula da yankin Mutunguru, Patrick Kimathi, ya bayyana cewa,gwamnati tana daukar kananan tashoshin samar da wutan lantarki ta hanyar amfani da karfin ruwa da muhimmanci matuka, bisa la'akari da makuden kudaden da ake kashewa, kayayyakin da ake amfani da su da kuma saukin sarrafa tashar.
Kimathi ya ce, da zarar an horas da al'ummomin yankunan karkara yadda za su kula da kuma cin gajiyar kananan tashoshin samar da hasken wutan lantarkin masu amfani da karfin ruwa da ke yankunan nasu, gwamnati a nata bangare za ta rika karbar kudin wutan da suke amfani da su, a wani mataki na kara samar da makamashi mai dorewa ,tsafta da kuma rahusa.(Ibrahim)