Francis Wangusi, shi ne daraktan hukumar sadarwa ta kasar Kenya, ya sanar da taron kolin na shiyyar ta shafin internet cewa, a halin yanzu kasashen Kenya, Uganda, Rwanda da Sudan ta kudu ne kasashe mambobin kungiyar da suke son dunkulewa waje guda.
Yace suna cigaba da tattaunawa da kasashen Tanzania da Burundi domin neman amincewarsu don shiga hanyar sadarwar ta bai daya, wanda zata bada dama a dinga biyan kudaden da ake caza na sadarwa daidai da kiran waya na cikin gida.
Kenya, Uganda, Rwanda da Sudan ta kudu sun kafa tsarin dunkulewar ne karkashin inuwar shirin samar da sadarwa na Northern Transport Corridor Network.
Kuma idan aikin ya kammala, hanyar sadarwa zata saukaka farashin kudaden kiran waya ga masu ta'ammali da wayoyin hannu ga al'ummar mambobin kasashen.
Wangusi, yace domin tabbatar da wannan aniya ta dunkulewar kasashen 6 na EAC don samar da hanyar sadarwa, akwai wasu matsalolin da ake saran warwaresu a kasashen Tanzania da Burundi da suka shafi sauya fasalin dokokin sadarwa na kasashen.(Ahmad Fagam)