Masanin ya ce, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, ta kara taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arzikin duniya. Musamman yayin da aka shiga karni na 21, kasar ta Sin ta kara bude kofarta ga kasashen ketare, abun da ya sa tattalin arziki gami da cinikayyarta suka samu bunkasa sosai. A halin yanzu, Sin na nuna kwazo wajen shiga harkokin cinikayya maras shinge a duk duniya, da gudanar da wasu muhimman ayyuka na inganta ababen more rayuwar jama'a a kasashe daban-daban, ciki har da gina hanyoyin mota, da tashoshin jiragen ruwa, da shimfida layin dogo da sauransu.
Har wa yau kuma, masanin ya ce, Sin tana taka rawa sosai a wasu muhimman tarukan duniya, kamar dandalin tattaunawar hadin-gwiwar Sin da Afirka, da kuma taron koli na kasashen BRICS. Sin tana taimakawa sosai wajen karfafa hadin-gwiwar kasa da kasa, musamman cude-ni-in-cude-ka tsakanin kasashen dake tasowa. A halin yanzu, kasar Sin na himmatu sosai wajen shiga ayyukan hadin-gwiwa da kasashe daban-daban a fannoni da dama.(Murtala Zhang)