Wakilin MDD a Somalia ya ce jazaman ne gudanar da zaben shugaban kasar a lokacin da aka tsara
Wakilin MDD a Somalia Micheal Keating ya ce dole ne a ba batun gudanar da zaben shugaban kasar Somalia a ranar da aka tsara muhimmanci, duk kuwa da kokarin kungiyar Al-Shabaab na kawo tsaiko, ciki har da hare-hare da kungiyar ta kai cikin makon nan da ya gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Ya kuma jadadda cewa, ya na da matukar muhimmanci tabbatar da gudanar da sahihin zabe kamar yadda doka ta tanada.
An dai yi ta dage ranar da aka shirya gudanar da zaben akai-akai, al'amarin da ya jefa damuwa a zukatan al'ummomin kasashen waje dake son a gudanar da zaben cikin wannan shekarar. ( Fa'iza Mustapha)