Shugaban hukumar gudanar da zaben shugaban kasar Abdirahman Dualeh Beileh, ya fada cikin wata sanarwa cewa, za a fara yin rajistar 'yan takarar shugabancin kasar ne tun daga yau Alhamis har zuwa ranar Lahadi mai zuwa.
Beileh yace 'yan takarar zasu gabatar da jawabai a gaban majalisun dokokin kasar daga ranar 2 zuwa 5 ga watan Fabrairu, kana a gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 8 ga watan Fabrairun.
Majalisar dokokin Somalia zata zabi shugaban kasar ne , kamar yadda dokar kasar ta bada dama ga 'yan majalisar su zabi wanda zai ja ragamar shugabancin kasar, zaben wanda da farko a shirya gudanar da shi a watan Satumba da Oktoba da Nuwamba daga karshe aka shirya yinsa a ranar 28 ga watan Disambar shekarar 2016, amma duk bai kai ga nasara ba.
A yanzu dai kwamitin shirya zaben kasar zai yi wasu muhimman taruka biyu a ranakun 30 ga watan Janairu da kuma 6 zuwa 7 ga watan Fabrairu, domin nazartar hanyoyin aiwatar da zaben shugaban kasar. A kalla sanatoci 17 da 'yan majalisar dokokin kasar ne aka zaba wadanda zasu halarci zaman tare da kwamitin shirya zaben.
Kasashen duniya da dama sun yi ta kiraye kirayen a gudanar da sahihin zaben shugaban kasar kuma mai inganci.