Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka gabatar a Mogadishu bayan kammala zabar shugabannin majalisun dokokin kasar, wanda wani muhimmin bangare ne na shirye shiryen zaben shugaban kasar, kungiyoyin na kasa da kasa sun bayyana cewa akwai gagarumin aiki kuma muhimmi dake gaban majalisun dokokin kasar.
Kungiyoyin na kasa da kasa sun hada da MDD, kungiyar tarayyar Afrika AU, data tarayyar turai EU, sun bayyna cewa dole ne majalisun dokokin su kaucewa duk wani abu da zai iya zubar da kimarsu wajen gudanar da zaben.
Kungiyoyin na duniya suna fatan majalisun dokokin na Somali zasu gudanar sahihin zaben shugaban kasar kuma mai inganci, wanda al'ummar kasar Somaliyan za su gamsu da shi dama kasashen duniya baki daya.
Wakilin musamman na MDD Michael Keating, ya bayyana cewa a yayin da Somali ke fama da dunbun matsaloli da suka hada da karancin abinci, rashin aikin yi, da rashin tsaro, ya kamata majalisar ta yi la'akari da yanayin da ake ciki wajen zabar mutumin da zai bada fifiko kan matsalolin dake addabar 'yan kasar ta Somaliya.(Ahmad Fagam)