Kawo yanzu dai ba a ayyana takamaiman lokacin da za a gudanar da zaben cikin watan na Janairu ba. Kaza lika wannan ne karo na hudu ana dage babban zaben kasar, wanda tun da fari aka tsara gudanarwa tun cikin watan Satumbar da ya shude.
Wasu al'ummun kasar dai sun nuna damuwarsu game da yawan dage babban zaben kasar, duk kuwa da kiraye kiraye da kasashen duniya ke yi, na ganin an gudanar da zaben a kan lokacin, kamar kuma yadda kundin mulkin kasar ya tanada. (Saminu Hassan)