Babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, ya jinjinawa matakin kaddamar da sabuwar majalissar dokokin kasar Somaliya, yana mai kira ga masu ruwa da tsaki a kasar, da su kara kaimi, wajen kammala ragowar zubukan kasar.
Cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, Mr. Ban ya ja hankalin sabbin 'yan majalissun, da su maida hankali ga nazartar muhimman dokoki, wadanda za su bunkasa dimokaradiyyar kasar, irin su dokar samar da kundin mulkin kasar na dindindin.
Kaza lika Ban ya bukaci mahukuntan kasar da su gaggauta cike gurbin dukkanin mukaman wakilcin al'umma da ake da su, tare da baiwa mata damar samun wakilci a majalissun kasar kamar yadda doka ta tanada. Ya ce ya dace a warware dukkanin wasu banbance banbance, da takaddama mai alaka da zaben wakilan jama'ar kasar cikin adalci, domin kare martabar dimokaradiyya.
An dai rantsar da 'yan majalissar dokokin kasar ta Somaliya su 284, wadanda suka hada da 'yan majalissar wakilai da na dattijai, a wani biki da ya gudana ranar Talata a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.(Saminu Alhassan)