Kakakin gwamnatin Mogadishu, Abdifitah Omar Halane, da ya tabbatar da adadin wadanda suka mutum, ya ce bam da ake tadawa da na'ura da aka binne a karkashin wata bishiya, da nufin kai hari kan sojojin dake hutawa a karkashinta.
Bam din ya tashi ne a wani wuri da ake ganinsa a matsayin mashigar Mogadishu, wanda zai kai ga wasu sassan kudancin kasar.
Wannan harin shi ne na biyu da aka kai a jiya Alhamis, domin sa'o'I kalilan kafin aukuwarsa, wasu mutane uku sun jikkata, sanadiyyar harin kunar bakin wake da wani ya kai a cikin mota, inda ya ajiye motar a wajen wani gidan cin abinci dake kusa da fadar shugaban kasar.
Tuni dai kungiyar Alshabaab ta dauki nauyin kai dukkan hare-haren biyu.
Hare-haren na zuwa ne a lokacin da ake sa ran 'yan majalisar dokokin kasar za su zabi sabon shugaban kasa a ranar 28 ga watan Decemba.
Kungiyar Al-shabaab na ta kaddamar da hare-hare a Somalia ne da nufin hambarar da gwamnatin kasar.
Don ko makonni uku da suka gabata, sai da wani hari da aka kai a gabar teku a birnin Mogadishu ya yi sanadin mutuwar mutane ashirin da tara.(Fa'iza)