Kakakin hukumar gudanarwar birnin Mogadishu, Abdifatah Omar Halane, ya shedawa 'yan jaridu cewa mayakan sun kashe mutanen biyu ne a daren Asabar din da ta gabata a gundumar Wadajir.
Dama dai tuni kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Al-Shabaab ta sanar da daukar alhakin kaddamar da harin, inda ta ce mayakanta ne suka kashe sojoji biyu tare da kwace wasu bindigogi 2 kirar AK47.
Al-Shabaab ta sha kaddamar da hare hare a kasar Somaliya a tsawon shekaru masu yawa sakamakon adawar da take da gwamnatin kasar.
Hare hare na baya bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke tsaurara tsaro a Mogadishu, domin gudanar da zaben shugaban kasar dake tafe a karshen wannan shekara. (Ahmad Fagam)