in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fara babban zaben shugaban kasar Somaliya a karshen watan Disamba
2016-12-11 13:43:46 cri
Bisa labarin da aka samu, an ce, an fidda wata sanarwa a yayin taron dandalin tattaunawar shugabannin kasar Somaliya, inda aka bayyana cewa, za a yi babban zaben shugaban kasar ta Somaliya a ranar 28 ga wannan watan na Disamba, haka kuma, kafin fidda wannan sanarwar, an sha dage babban shugaban kasar a sau da dama.

Haka kuma, bisa sanarwar da aka fidda a ran 8 ga wata, an ce, a ranar 25 ga wata, mambobin majalisar dattijai da majalisar wakilai za su yi rantsuwar kama aiki, sa'an nan, za a gudanar da zaben shugaban majalisar dattijai da shugaban majalisar wakilai a ran 22 ga watan nan da muke ciki.

Kaza lika, bisa kundin tsarin mulkin kasar Somaliya na rikon kwarya, an ce, mambobin majalisar wakilai 275 da mambobin majalisar dattijai 54 za su zabi shugaban kasar ta Somaliya cikin hadin gwiwa.

Tawagar gudanar da babban zaben kasar Somaliya ta taba bada sanarwa a ranar 8 ga wata cewa, za a gudanar da babban zaben shugaban kasar a ranar 30 ga watan Oktoba, sa'an nan, aka jinkirta babban zaben zuwa ranar 30 ga watan Nuwanba.

Kana, bisa labarin da aka samu, an ce, mai iyuwa ne, tashe-tashen hankulan da kungiya mai tsattsauran ra'ayi a kasar Somaliya ta Al-Shabab ta sha yi a kasar, da kuma sabanin dake tsakanin kabilu daban daban da yankuna daban daban a kasar Somaliya sun haddasa jinkirta babban zaben shugaban kasa ta Somaliya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China