in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha: Bai kamata a soke izinin gudanar da gasannin duniya a kasar ba
2016-12-15 10:29:19 cri
A jiya Laraba 14 ga watan nan ne sakataren yada labarai na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov, ya yi zargin cewa dalilan siyasa ne suka sanya aka soke izinin Rasha na gudanar da gasannin duniya.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai kungiyar IBSF (International bobsleigh and skeleton Federation) ta fidda sanarwar soke shirin da aka yi na gudanar da gasar bobsleigh da ta skeleton ta shekarar 2017 ta duniya a birnin Sochi na Rasha, inda ta ce nan gaba za a bayyana sabon wurin da za a gudanar da gasannin.

Rahotanni na cewa hukumomin bobsleigh da skeleton na kasashen Latvia da Koriya ta Kudu da sauransu, da wasu 'yan wasa daga Birtaniya da Amurka, da suka samu lambobin yabo a gasar wasannin Olympics sun nuna rashin amincewa da gudanar gasar a Rasha, domin nuna kiyayyar su da batun abun kunyan nan na amfani da kwayoyin kara kuzari da ake zargin 'yan wasan Rasha da aikatawa.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China