Kremlin: Gyara dangantaka tsakanin Rasha da Amurka ba zai kasance cikin sauki da sauri ba
Sassanta Rasha da Amurka a karkashin jagorancin sabuwar gwamnatin Donald Trump ba zai kasance wani shiri mai sauri da sauki ba, in ji Kremlin a ranar Laraba. Kakakin fadar ta shugaban kasar Rasha, Dmitri Peskov ya bayyana a gaban manema labarai cewa, wannan huldar dangantaka ta kai makura a karkashin gwamnatin Barack Obama. A yayin da hukumomin Moscou suke fatan ganin sake maido da tattaunawa tare da Washington, mista Peskov ya jaddada cewa zai kasance shiri mai mutukar wuya kuma ga dukkan alamu ba mai sauri ba. (Maman Ada)