Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana jiya Laraba, cewar bayan da aka kammala babban zabe a kasar Amurka, Rasha na da imanin cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu za ta samu kyautatuwa.
Bisa labarin da aka samu daga tashar Intanet ta fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin, an ce, yayin da shugaba Putin ke halartar wani taron dandanlin tattaunawa a wancan rana, ya furta cewa, Rasha da Amurka ba za su iya tinkarar kalubaloli iri daban daban da ke gabansu a halin yanzu ba, idan babu kasancewar dangantakar abokantaka a tsakaninsu yadda ya kamata.
Putin ya kara da cewa, abin bakin ciki shi ne, a 'yan shekarun baya baya nan, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu tana ta kara kamari, amma wannan ba laifin kasar Rasha ba ne. Yanzu an riga an kammala babban zabe a Amurka, kuma za a samu wani sabon shugaban kasar. Don haka, Rasha na da imanin cewa, wannan zai zama wata kyakkyawar dama wajen kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wanda kuma za ta ba da muhimmin tasiri wajen kawo alheri ga jama'arsu da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Bugu da kari, Putun ya bayyana cewa, ya buga wayar tarho ga shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump a kwanan baya, inda bangarorin biyu suka tabbatar da wajibcin kyautata dangantakar da ke tsakanin Rasha da Amurka. (Kande Gao)