Bayan da Obama ya gana da firaministar kasar Birtaniya Theresa Mary May, da shugaban kasar Faransa François Hollande, da firaministan kasar Spaniya Mariano Rajoy da firaministan kasar Italiya Matteo Renzi da shugabar gwamnatin Jamus Merkel ya bayar da sanarwa cewa, dukkan shugabannin kasashen 6 suna ganin cewa, idan kasar Rasha ba ta aiwatar da yarjejeniyar Minsk ba, tilas ne a tabbatar da kakabawa Rashar takunkumi, da nuna goyon baya ga tsawaita wa'adin saka takunkumin.
Sanarwar ta kara da cewa, ana nuna damuwa game da rashin tsagaita bude wuta a dogon lokaci, tilas ne a tabbatar da yin tsari game da rikicin kasar Ukraine, da kuma gudanar da zabe cikin adalci a jihohin Donetsk da Luhansk da sauran jihohin dake gabashin kasar Ukraine.(Zainab)