Shugaba Putin, ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su mika rahoto ga babban sakataren MDD kan wannan batu, domin sanar da cewa Rashar ba ta da niyyar cigaba da zama mamba ta yarjejeniyar Rome ta kotun ICC. Bugu da kari a cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar, ta tabo batun musamman kan yakin dake tsakanin Rasha da Georgia a watan Agusta na shekarar 2008, tare da nuna rashin amincewa da matsayin da kotun ta Hague ta dauka kan wannan batu.
Kasashen Burundi, da Afirka ta Kudu, da kuma Gambiya sun riga sun sanar da ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a karshen watan Oktoban bana, inda suka zargi kotun da zama yar koron kasashen yammacin duniya wajen nuna bambanci ga kasashen Afirka.(Fatima)