A jiya Laraba ne, taron koli na zuba jari a Afrika karo na uku ya yi kira da a kawar da cin hanci da karbar rashawa a Afrika, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar masana'antu a nahiyar.
Masana mahalarta taron sun tattauna kan yadda za a warware matsalar cin hanci da karbar rashawa, inda suka mai da hankali kan bukatar nuna adalci da tsarin sa ido kan jami'ai.
A jawabinsa ministan kasuwanci da masana'antu na kasar Ruwanda Francois Kanimba ya bayyana cewa, wasu matakai masu yakini da ake dauka za su ciyar da sha'anin masana'antu a nahiyar Afrika gaba, ciki hadda yaki da cin hanci, bunkasa cinikayyar shige da fice, bunkasuwar al'umma, sayar da kimiyya da fasaha, zuba jari kai tsaye daga kasashen waje da kuma kara raya muhimman ababen more rayuwa.
Kididdigar da bankin raya Afrika ya fitar na nuna cewa, a ko wace shekara nahiyar Afrika tana hasara kudaden da suka kai dala biliyan 148 sanadiyar matsalar cin hanci da karbar rashawa. (Amina)