Taron na tsawon mako guda ya tantance bukatu daban daban na kasashen Afrika domin rage yadda ya kamata fari da kuma bunkasa wani sahihin tsari da zai taimaka wajen kara juriya ga matsalar fari. Sanarwar Windhoek kan juriya ga fari ta samu rattaba hannun shugabannin kasashen da suka halarci taron.
Mahalartan taron sun jadadda wajabci ga Afrika na kafa wani asusun da zai kula da rage fari da kuma kafa wani kwamitin da zai kula da aiwatar da kuduran da taron ya cimma.
Shugaban Namibiya, Hage Geingob ya jaddada a ranar Alhamis da ta gabata kan muhimmancin halartar bangaren masu zaman kansu da kuma kungiyoyin fararen hula domin shiga gaban matsalar fari.
Ana bukatar dalar Amurka kimanin biliyan uku domin taimakawa kasashen da matsalar fari ta shafa dake cikin kungiyar kasashen SADC. (Maman Ada)