Wani jami'in gwamnatin kasar jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya ya bayyana cewa, masu fafutuka sun kaddamar da hare-hare kan birnin Kaga-Bandoro, birnin dake tsakiyar kasar da kuma wasu kauyukan dake dab da birnin, tsakanin daren ranar 16 ga wata zuwa ranar 17 ga wata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 20, yayin da wasu da dama suka ji rauni, kuma kawo yanzu ba a tantance dalilin kaddamar da hare-haren ba tukuna.
An ba da labarin cewa, kasar jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya ta dade tana cikin mawuyacin hali mai sarkakiya, inda mambobin kungiyar masu dauke da makamai ta Anti-Balaka, da na tsohuwar kungiyar Seleka ke fito-na-fito da juna, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai mai tsanani a kasar. (Amina)