in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ba za ta dauki fansa kan sabon takunkumin da za a iya sanya mata ba, in ji firaministan kasar
2016-11-06 13:05:57 cri

Firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev ya ce, kasarsa ba za ta dauki fansa kan sabon takunkumin da kungiyar Tarayyar Turai da kasar Amurka za su iya sanya mata ba, saboda irin wannan ja in ja game da sanya takunkumi a tsakanin sassa biyu ba ta da amfani.

Mista Medvedev ya fadi haka ne yayin da yake zantawa da wakilin gidan telibijin na biyu na kasar Isra'ila a ranar 5 ga wata, inda ya kara da cewa, Rasha a shirye take wajen farfado da huldar da ke tsakanita da Amurka nan take, sai dai abin ya danganta da matsayin da sabuwar gwamnatin Amurka za ta dauka bayan babban zabe. Duk wanda ko wadda ya ci zaben, Rasha a shirye take wajen bunkasa kyakkyawar hulda a tsakanin kasashen 2, bisa tanade-tanaden dokokin kasa da kasa, da ka'idar samun ci gaban kasa da kasa bai daya a duniya, kuma bisa matsayinsu na kasashen dake da kujerar din din din a kwamitin sulhu na MDD da kuma kasashen dake da makaman nukiliya.

Tun bayan watan Maris na shekarar 2014 har zuwa yanzu, kasar Amurka da kungiyar Tarayyar Turai suka fara sanya wa kasar Rasha takunkumi dangane da batun kasar Ukraine, yayin da ita ma Rashan ta mayar da martani kansu. A 'yan kwanakin da suka gabata, sabanin da ke tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya ya kara tsananta sakamakon batun kasar Syria. Akasarin ra'ayoyin jama'a sun yi hasashen cewa, mai yiwuwa ne kasashen yammacin duniya za su garkama wa Rashan sabon takunkumi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China