Kotun yanke hukunci kan harkokin wasannin motsa jiki na kasa da kasa ta yi watsi da karar da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu na Rasha ya gabatar masa kan hukuncin da aka yanke game da hana kasar shiga gasar Olympics ta nakasassu, saboda haka kila Rasha ba za ta halarci wannan gasa ba da za a yi a birnin Rio.
A ranar 7 ga wata ne kwamitin shirya gasar Olympics ta nakasassu na kasa da kasa ya sanar cewa, za a hana Rasha shiga gasar saboda Rasha ta gaza aiwatar da tsarin hana yin amfani da magunguna kara kuzari na kasa da kasa da tanade-tanaden kwamitin gasar Olympic ta nakasassu dake da nasaba da hana yin amfani da magunguna. Wannan ya sa Rasha ta shigar da kara, amma kotun kula da harkokin wasannin motsa jiki ya ba da sanarwa a jiya bayan ya kira wani taron tattara shaida a ranar Litinin a birnin Rio, inda ya sanar da cewa, alkalai suna ganin cewa, shawarar da kwamitin ya yanke kan Rasha na hana ta shiga gasar a makoni biyu da suka gabata ya yi daidai, a saboda haka an yi watsi da karar da Rasha ta shigar. (Amina)