An kwashe fasinjoji daga wani jirgin sama a filin jiragen saman Geneva bayan wani gargadin bam
Wani jirgin saman kamfanin jiragen saman na Rasha an kwashe mutane daga cikinsa a ranar Alhamis jim kadan kafin ya tashi daga filin jiragen sama na Geneva zuwa Moscou, bayan wani gargadin bam, in ji ma'aikatar jama'a ta Geneva, wata hukumar shari'a ta Geneva, a cikin wata sanarwa. Dukkan fasinjojin 115 dake cikin jirgin saman mai lamba 2381 an kwashe su baki daya, kuma babu wanda ya ji rauni. Ma'aikatan dake lalata boma bamai na 'yan sandan wurin suna yi wa jirgin saman bincike kwakwab domin gano duk wata bom dake cikin jirgin. Bisa matakin riga kafi, jirgin saman dake shirin tashi an mayar da shi a wurin tsayuwarsa sannan aka fitar da dukkan fasinjojin dake cikinsa. Fasinjojin zasu shiga wani jirgin saman na daban domin cigaba da tafiye tafiyen su, in ji kamfanin jiragen saman na Rasha a cikin wata sanarwa. (Maman Ada)