Ahmad Majdalani, mamban kwamitin zartaswa na OLP, ya jadadda cewa fadar Kremlin ba ta aike da takardar gayyata ba, amma ta bukaci hukumar Falasdinawa da ta shirya kan wannan dandalin na bangarori uku.
An sami labarin daga Rasha cewa tana maida hankali sosai kan dukkan shirye shiryen ganawa tare da Netanyahou, tare da kawar da dukkan shingayen dake kan hanya kafin a aike da takardun gayyata a hukumance, in ji jami'in.
Jami'in ya kara da cewa faraministan Rasha Dmitri Medvedev, zai isa Isra'ila da gabar yamma ta kogin Jordan a ranar 10 ga watan Nuwamba, domin tattaunawa kan wannan batu.
Ahmad Majdalani ya bayyana cewa bangaren Palesdinu a shirye yake ga duk wata ganawa tare da bangaren Isra'ila idan har wannan ganawa zata gudana cikin gajeren lokacin da aka tsaida kuma zata taimaka wajen samar da sakamako mai kyau. (Maman Ada)