in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha da Amurka sun cimma matsayi kan aiwatar da sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Syria
2016-09-11 13:23:39 cri
Jiya Asabar, ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov, sun cimma matsayi game da batun aiwatar da sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin bangarori daban daban da ricikin kasar Syria ya shafa, sun tattauna wannan batu ne a birnin Geneva, domin ba da taimako ga kasar Syria wajen warware wannan matsala ta hanyar siyasa kuma cikin sauri.

Dangane da wannan lamari, manzon musamman na babban magatakardan MDD dake kula da batun Syria mista Staffan de Mistura ya fidda wata sanarwa a ranar 10 ga wata, inda ya yi maraba da matakan da kasashen Amurka da Rasha suka dauka na cimma matsayi guda kan sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Syria da kuma yadda za su hada kai wajen yaki da 'yan ta'adda dake kasar Syria, haka kuma, ya sa kaimi ga bangarorin da rikicin kasar Syria ya shafa, da su yi amfani da wannan dama domin warware matsalar ta hanyar siyasa cikin hanzari.

Bugu da kari, gwamnatin kasar Syria ta nuna goyon baya ga kasashen Amurka da Rasha da suka cimma matsayi daya kan aiwatar da sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin bangarori daban daban da ricikin kasar Syria ya shafa.

Haka zalika, kungiyar tarayyar Turai, da kasashen Burtaniya, Faransa, Turkiyya da wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama, sun yi maraba da wannan mataki domin ganin yadda za a ciyar da ayyukan warware ricikin kasar Syria ta hanyar siyasa gaba, bayan da kasashen biyu suka cimma ra'ayi daya kan aiwatar da sabuwar yarjejeniyar.

A yayin taron manema labarai da aka yi a birnin Geneva a jiya Asabar 11 ga wara, John Kerry ya ce, bisa ra'ayi daya da kasashen Amurka da Rasha suka cimma, an ce, gwamnatin kasar Syria za ta dakatar da bude wuta ga dakarun jam'iyyun adawa, a sa'i daya kuma, ya kamata dakarun jam'iyyun adawar su dakatar da bude wuta ga sojojin gwamnatin, sannan ya zama tilas su yanke alaka a tsakaninsu da 'yan ta'adda dake kasar Syria.

Idan za a iya aiwatar da sabuwar yarjejeniyar ta tsawon kwanaki 7, to, kasashen Amurka da Rasha za su karfafa hadin gwiwar harkokin soja dake tsakaninsu a kasar Syria, ciki har da tsara shirin yaki da 'yan ta'adda a kasar Syria cikin hadin gwiwa.

Haka kuma, bisa lokacin da aka tsara, za a fara aiwatar da sabuwar yarjejeniyar ne daga ranar 12 ga wannan wata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China