Kakakin fadar shugaban kasar Sudan ta Kudu Ateny Wek Ateny ya ce, dole sai an cimma nasarar dakatar da bude wuta kafin a yi batun gudanar da sauye-sauye a kasar.
Mr. Ateny na mai da martani ne ga zargin da tsagin masu adawa da gwamnatin kasar suka yi, cewa gwamnatin shugaba Rick Machar na adawa da sauye-sauyen da ka iya ciyar da kasar gaba.
A watan Yulin da ya gabata ne dai fada ya sake barkewa tsakanin dakarun gwamnati da tsagin 'yan tawaye karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar, lamarin da ya raba dubban 'yan kasar da gidajen su.
Kakakin Mr. Machar James Gatdet Dak, ya ce da ma dai an kafa gwamnatin hadakar kasar ne da nufin aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya, wadda kungiyar IGAD ke marawa baya.
Shi ma kakakin gwamnatin Sudan ta Kudu cewa ya yi, cikin wadannan manufofi had da tsara sabon kundin mulkin kasar, da ma gudanar da sauye-sauye a fannin tsaro. (Saminu)