Malam Kiir ya bayyana haka ne a jiya yayin da sabon jakadan kasar Sin dake kasar Sudan ta Kudu He Xiangdong ya mika masa takardarsa ta aiki, inda ya kuma yi masa maraba da zuwa kasarsa a matsayin sabon jakadan kasar Sin.
Ya ce, kasar Sudan ta Kudu tana mai da hankali matuka wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, tana kuma fatan karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin man fetur, gina ababen more rayuwa, harkar noma, samar da wutar lantarki da dai sauransu.
Haka zalika, ya nuna godiyarsa ga kasar Sin dangane da taimakon jin kai da ta baiwa kasarsa, yana kuma fatan kasar Sin za ta kara taimakawa kasar Sudan ta Kudu a kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar kasa.
A nasa bangare, He Xiangdong ya bayyana cewa, tun bayan da kasashe Sin da Sudan ta Kudu suka kulla dangantakar diflomasiyya, shekaru biyar da suka gataba, dangantakar kasashen biyu take ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau, kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma tana son ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sudan ta Kudu don inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)