Kakakin rundunar sojan kasar Lul Rui Koang, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, an yi fama da tashin hankali a garin Morobo a 'yan kwanakin baya, amma daga bisani al'amura sun lafa.
Tun farko mai magana da yawun Machar, James Gatdet Dak ya tabbatar da cewa, dakarunsu sun kwace iko da garin Morobo da ke kusa da garin Yei wanda ya yi fama da fadan da ya barke tsakanin dakarun gwamnati da na Machar a farkon watan Yuli
Koda ya ke Koang ya bayyana cewa, sojoji sun bude hanyar Juba zuwa Yei wadda ta hade yankunan Kaya da Morobo da ke kusa da kan iyaka da kasashen Uganda da Jamhuriyar demokiradiyar Congo.(Ibrahim)