Mataimakin babban sakataren MDD na musamman a Sudan ta kudu Eugene Owusu, ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen sake gina al'umma, samar da kayayyaki ga wadanda ke matukar bukata, sake farfado da tattalin arzikin kasar, farfado da gine-gine da sauran muhimman kayayyaki.
Owusu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kaddamar da shirin hadin gwiwar MDD na wucin gadi(ICF) na tawagar MDD da ke Sudan ta kudu, tawagar da ke kasar da nufin samar da ci gaba a kasar dake fama da koma baya.
Yakin basasan da aka shafe sama da shekaru biyu a na gwabzawa a kasar, ya jefa ta cikin wani hali, inda hauhawar farashin kaya ta kai kashi 663 cikin 100.(Ibrahim)