Matsalar tsaro a Yei ta kara tsananta cikin sauri bayan barkewar rikici a Juba a farkon watan Yulin da ya gabata, lamarin da ya tilastawa miliyoyin fararen hula barin gidajensu, in ji HCR a cikin wata sanarwa.
Dakarun dake karkashin shugaba Salva Kiir da wadanda suke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar sun yi kazamin fada a farkon watan Yuli a Juba, lamarin da ya janyo sauran tashe tashen hankali a cikin kasar.
A cewar HCR, wannan ne karo na farko da mazauna Yei, musammun ma manoma, suka zama mutanen da aka kaiwa hari kai tsaye game da tashe tashen hankalin.
Mazauna Yei sun yi magana kan muguwar azabatarwa da ake yi wa fararen hula, har ma da hare hare, da kisan mutane, sace dukiyoyin jama'a da kona gidaje, a cewar HCR.
Haka kuma hukumar ta bayyana cewa mutanen da suka kaura, da kuma mazauna wurin dubu 60 da suka tsaya Yei, suna bukatar agajin jin kai.
Mutanen da suka kaura suna bukatar abinci, kayayyakin bukatun yau da kullum, magunguna, kuma ya kamata yara su shiga makaranta. Kayayyakin abinci sun yi tashin gobron zabo, tare da kayayyakin bukatun da yau da kullum na bacewa cikin sauri a cikin kasuwanni, in ji sanarwar HCR. (Maman Ada)