Ministan ciniki da masana'antu na kasar Rob Davies ya ce, Jami'an su ne ke da alhakin gudanar da shirin SEZs a Afrika ta kudu.
Davies ya ce, Africa ta kudu ta bullo da shirin na SEZs ne domin bunkasa masana'antu a wani mataki na tunkarar kalubalen dake addabar tattalin arzikinta, da suka hada da rashin aikin yi, da koma bayan cigaba a kasar.
Daga cikin yarjejeniyar da aka cimma da Afrika ta kudu a shekarar 2014, a duk shekara, za'a horas da jami'ai kimanin 30 ne a nan kasar Sin.
Davies ya ce ana sa ran shirin zai baiwa jami'an kwarewa game da shiryawa da aiwatar da shirin na SEZs.
Shirin dai ya kunshi batutuwa da suka hada da ba da horo kan samar da ababan more rayuwa, da dabarun kasuwanci, da zuba jari, da kuma tara kudade domin shirin na SEZs. (Ahmad Fagam)