in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Afrika ta kudu ya sake ba da gargadin rigakafin harin ta'addanci
2016-06-05 13:04:39 cri
Ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Afrika ta kudu ya sake ba da gargadin rigakafin harin ta'addanci, inda ya ce, ya samu bayanin leken asiri cewa, 'yan ta'adda suna shirya kai hare-hare ga matsugunan Amurkawa dake kasar Afrika ta kudu.

Wannan bayanin ya nuna cewa, watakila za a kai hare-hare wasu wuraren biranen Johannesburg da Cape Town.

Kakakin ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Afrika ta kudu ya bayyana cewa, kasar Amurka tana yin hadin gwiwa tare da Afrika ta kudu wajen gudanar da bincike kan batutuwan ta'addanci.

A watan Satumba na shekarar bara, ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Afrika ta kudu ya ba da gargadin rigakafin harin ta'addanci, ya kuma fayyace cewa, 'yan ta'adda za su kai hare-hare ga Amurkawan dake kasar. Sai dai a lokacin ma'aikatar tsaron Afrika ta kudu ta ce, babu bayanin da ta samu da ya sheda cewa, za a kai harin ta'addanci a kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China