Ministar ilimi na kasar Afrika ta kudu Angie Motshekga, ta ce jami'o'i 15 dake jihohi 4 a kasar, sun fara koyar da darussan Sinanci tun daga watan Janairu na wannan shekara. Kuma cikin shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin kasar ta shirya kaddamar da wannan darassi a jami'o'i 500 na kasar, domin kara samar da damar koyon Sinanci ga jama'a.
Angie Motshekga wadda take amsa tambayoyin 'yan majalissun kasar, ta ce jami'o'in dake koyar da Sinanci na kasar Afrika ta kudu sun kasance a jihohin Western Cape, da East Cape, da Gauteng, da kuma KwaZulu-Natal, kuma nan gaba za su habaka zuwa sauran jihohi 5.(Lami)