A cewar wannan rahoto, jimilar GDP na Najeria ta kai dala biliyan 296, a yayin da wannan jimila ta kai dala biliyan 301 a Afrika ta kudu bisa tsarin canjawa kudi na yanzu.
A cikin shekaru biyu da suka gabata, Najeriya ta ba da kididdiga cewa, ta kai matsayi na farko a fannin tattalin arziki, amma bayan sake yin sabuwar kididdiga bisa tsarin canjin kudi a yanzu haka, sakamakon ya nuna cewa, Afrika ta kudu ta maye gurbinta, tare da rike matsayi na farko. An gudanar da wannan kididdiga ne bisa jimilar GDP ta kasashen biyu a shekarar 2015.
Nijeria ta sake yin kididdiga kan GDP dinta a shekaru biyu da suka gabata, wadda ta shigo da wasu sana'o'i da ba su shiga cikin kididdigar a baya ba, ciki hadda sana'ar sadarwa, kimiyyar labarai, wake-wake da kide-kide, saye da sayarwa a kan Intanet, zirga-zirgar jiragen sama, da fina-finai da dai sauransu, ta yadda Nijeria ta wuce Afrika ta kudu.
Amma kwanan baya darajar Naira ta ragu sosai yayin da kudin Afrika ta kudu Rand ya karu, dalilin da ya sa GDP Nijeria ya ragu. (Amina)