A yayin bikin bude ofishin a Kenya, mista Chi Jianxin, babban darektan asusun CAD, ya bayyana cewa, kafa wannan ofishi zai taimakawa kamfanonin kasar Sin wajen habaka harkokinsu da kara zuba jari a kasashen Afirka daban daban.
Ya zuwa karshen watan Agustan bana, asusun CAD ya riga ya zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 3.5 don tallafawa manyan ayyuka 87 da ake gudanar da su a kasashe 36 dake nahiyar Afirka, wadanda suka shafi hadin gwiwa a fannin masana'antu, kayayyakin more rayuwa, hakar ma'adinai, aikin gona da dai makamantansu. Ta wadannan ayyuka, an samu damar amfanawa jama'ar kasashen Afirka da yawansu ya kai fiye da miliyan 1, tare da sa kaimi ga kamfanonin Sin da su kara zuba jari a Afirka.(Bello Wang)