Jami'an diflomasiyar sun nuna cewa, ba mai kawai wannan layin dogon zai taimaka wajen raya tattalin arzikin kasar Kenya ba, hatta ma zai ciyar da tattalin arzikin sauran kasashe dake gabashin Afrika gaba. Haka kuma yana da muhimmanci sosai wajen cimma burin muradun nahiyar Afrika na shekarar 2063 da tabbatar da sakamakon da aka samu a taron kolin dandanlin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika(FOCAC) da aka yi a Johnnesberg na kasar Afirka ta kudu
Ban da wannan kuma, an yi hasashen cewa, wannan layin dogo zai taimakawa ci gaban GDPn kasar Kenya da kashi 1.5 bisa dari, da kuma ciyar da tattalin arziki da sauran fannonin rayuwa gaba, da sa kaimi ga cinikayyar shige da fice ta kasar Kenya. Haka kuma aikin gina layin dogon ya samar da guraben aikin yi fiye da dubu 30, matakin da ya taimaka wajen warware matsalar rashin aikin yi da ake fama da ita a wurin. (Amina)