Ministan harkokin majalissar ministocin kasar Sudan ta Kudun, Martin Elia Lomoro, shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa domin kyautata yanayin tsaro a kasar, gwamnati ta riga ta amince da kudurin kwamitin sulhun MDD na jibge sojojin wanzar da zaman lafiya.
A ranar 2 ga wata, tawagar kwamitin sulhun MDD ta isa birnin Juba, helkwatar kasar Sudan ta Kudun, domin nazartar yanayin tsaro da ake ciki a kasar. Rahotanni na cewa bayan ganawar shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit da tawagar kwamitin sulhun MDD a ranar 4 ga wata, gwamnatin kasar ta amince da wannan kuduri.
Mr. Lomoro ya kara da cewa, gwamnatin Sudan ta Kudu za ta tattauna da wakilan kwamitin sulhun game da yadda za a jibge wadannan sojojin wanzar da zaman lafiya 4000. A sa'i daya, gwamnatin kasar za ta tsara wani shiri tare da tawagar MDD a Sudan ta Kudun, za kuma a dauki kwararan matakai, na kara kawar da shingen da tawagar MDD za ta iya fuskanta wajen gudanar da aikinta a Sudan ta Kudun. (Fatima)