in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sudan ta Kudu tana son yin shawarwari kan shimfida rundunar sojan kiyaye tsaron yankin
2016-08-16 13:21:16 cri
A jiya Litinin 15 ga wata, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son tattaunawa da MDD da sauran kasashen dake yankin kan batun jibge rundunar sojan kiyaye tsaron yankin.

Mr.Kiir ya bayyana haka ne a yayin bikin bude majalisar dokokin kasar ta wucin gadi, haka kuma, ya ce, gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ba ta yanke shawara ta karshe ba, kan kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya cimma, kuma bai kamata a matsa wa gwamnatin kasar lamba ba kan wannan batu, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su yi shawarwari domin warware batun.

A ran 12 ga wata ne, kwamitin sulhu na MDD ya tsai da kuduri kan kara adadin sojoji da za a tura zuwa kasar Sudan ta Kudu zuwa dubu 17, ciki har da sojojin kiyaye tsaron yankin dubu 4.

Bayan da aka zartas da wannan kuduri a kwamitin sulhu na MDD, zaunannen wakilin kasar Sudan ta Kudu dake MDD Akuei Bona Malwal ya yi jawabi cewa, an yake kudurin ba tare da sauraron ra'ayin kasar Sudan ta Kudu ba, shi ya sa, gwamnatin kasar ba ta aimince da kudurin ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China