A wannan rana, kwamitin sulhun MDD ya jefa kuri'a kan daftarin kudurin da aka kyautata bisa bukatun tawagar musamman ta MDD kan batun Sudan ta Kudu, inda aka zartas da kudurin bisa kuri'ar amincewa 11, da kuri'ar janye jiki 4. Kasashen Sin da Rasha da Masar da kuma Venezuela sun jefa kuri'ar janye jiki. Zaunannen wakilin Sudan ta Kudu a MDD, Bona Malwal ya bayyana bayan zartas da kudurin cewa, wannan kuduri bai yi la'akari da ra'ayin gwamnatin Sudan ta Kudu ba kan batun jibge sojojin wanzar da zaman lafiya a shiyyar da sauran wasu batutuwa, shi ya sa gwamnatin kasar ba za ta amince da kudurin ba.
A cikin jawabinsa, Liu Jieyi ya bayyana cewa, game da batun Sudan ta Kudu, kasar Sin tana fatan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar cikin sauri, da sassauta illolin da yanayin Sudan ta Kudu ke kawo wa kasashen dake wannan shiyya yadda ya kamata.(Fatima)