A kwanan baya ne, kungiyar bunkasa gwamnatocin kasashen gabashin Afirka (IGAD) ta fidda rahoton taron koli na musamman kan yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudu, inda aka amince da tura sojojin ba da kariya zuwa Sudan ta Kudu.
Game da wannan batu, madam Hua ta bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da kokarin da kasashen dake shiyyar da bangarori daban daban na Sudan ta Kudu suka yi domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Da fatan bangarorin za su gagauta cimma matsaya daya ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, a kokarin ganin an sassauta yanayin da ake ciki a kasar. Sin na fatan ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Sudan ta Kudu.(Fatima)