Wata majiya ta ofishin ministan gidan na Benin, ta bayyana hakan bayan hukuncin da kotun kolin shari'a ta kasa da kasa (CIJ) ta yanke game da rikicin kan iyaka da ke tsakanin Benin da Nijar, amma kuma har yanzu kasar ta Benin na fama da matsalolin iyaka tare da makwabtanta kamar Burkina Faso, Togo, da Najeriya, duk da cewa kasar na shirin gabatar gaban kotun CIJ da wasu shaidun da ke tabbatar da iyakokin ta. Kasar Benin na raba kan iyakoki bisa tsawon kilomita 1,989 tare da kasashe makwabtanta, wanda kuma ruwa, da duwatsu suka nuna shaidar iyakar ko wace kasa, dalilin haka ne, kasar take raba iyaka bisa tsawon kilomita 306 da Burkina Faso, kilomita 266 da Nijar, da kuma raba yankin ruwa, bisa tsawon kilomita 773 da Najeriya, da kilomita 644 da Togo.(Laouali Souleymane)