in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta soke takarar visar shiga ga 'yan Afrika
2016-08-31 10:38:01 cri
Da yake ziyarar aiki a kasar Rwanda, shugaban kasar Benin Patrice Talon ya sanar a ranar Litinin da yamma kan soke takardar neman izinin shiga Benin ga dukkan 'yan Afrika domin bunkasa yawon bude ido na Afrika da kuma dangantaka tsakanin kasashe masu tasowa, in ji gidan talabijin kasar Benin a ranar Talata.

Shugaban kasar Benin, da yake jawabi a yayin wata liyafa da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame ya shirya masa, ya tabbatar da cewa yana koyi da kwarewar Rwanda a wannan fanni.

"Bisa koyin da nike da kasar Rwanda, na dauki niyyar cewa kasar Benin ba za ta tilasta takardar neman izinin shiga ba ga 'yan Afrika. Dangantakar kasashe masu tasowa za ta dauki ma'anarta sosai. Fatana shi ne dangantaka tsakanin Rwanda da Benin ta kasance wani abin koyi", in ji mista Patrice Talon.

Baya ga mutanen kasashe mambobin kungiyar gamayyar tattalin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), baki 'yan kasashen waje har ma da na wasu kasashen Afrika dake son zuwa Benin dole har zuwa yanzu sai sun tanadi takardar neman izinin shiga.

Mista Talon na ziyarar aiki tun daga ranar Litinin a Kigali bisa burin kara karfafa huldar dangantaka tare Rwanda, musamman ma a fannonin zuba jari da kasuwanci.

Kasashen Benin da Rwanda, sun rattaba hannu a cikin watan Maris din da ya gabata a birnin Cotonou, hedkwatar tattalin arzikin Benin, kan wata yarjejeniyar zirga zirgar jiragen sama dake hasashen bude a ranar 2 ga watan Satumba da zirga zirgar jiragen saman kamfanin RwandaAir zuwa Cotonou. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China