Babban sakatare a fadar shugaban kasar Benin Pascal Koupaki ya shaidawa taron manema labarai cewa, sakaci da rashin bin ka'idojin aiki ne suka haddasa fashewar ta ranar 8 ga watan Satumba.
Ya ce, binciken farko da aka gudanar sun tabbatar da cewa, ba a samu izni ba kafin a gudanar da aikin kona sharar, sannan ba a bi ka'idojin da aka gindaya na kona kayayyakin da suka lalace ba, sannan ba a tanadi matakan kaucewa aukuwar hadarin ba.
Koupaki ya ce, ya zuwa yanzu gwamnati ta kori manyan jami'ai guda 3, ciki har da babban jami'in 'yan sandan yankin, bisa laifin sakaci da ayyukansu, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da jikkatar mutane.
Ya ce, baya ga wannan hukunci, gwamnati ta umarci ministan shari'a na kasar da ya hanzarta gudanar da bincike na shari'a da nufin hukunta duk wanda ke da hannu a wannan bala'i. (Ibrahim Yaya)