Shugaban Benin zai kawo ziyarar aiki a kasar Sin
Shugaban kasar Benin, Patrice Talon, a karkashin wata muhimmiyar tawaga, zai halarci a ranar Laraba zuwa ranar Alhamis, wani dandalin zuba jari a Afrika karo na biyu da za a bude a birnin Guangzhou, dake kudancin kasar Sin. Wannan haduwa ta kasance wani shirin da gwamnatin Sin ta kirkiro tare da tallafin hukumomin kudin kasa da kasa, dake da manufar tattara a kowace shekara masu ruwa da tsaki daban daban daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu na kasar Sin da Afrika, da wakilan hukumomin kudi na kasa da kasa, da abokan huldar ci gaba, domin ba su wata damar zurfafa shawarwari kan siyasa, musanyar kwarewa da tattauna hanyoyin da za su taimakawa wajen ba da kwarin gwiwa da rakiyar zuba jari da kuma ci gaba mai karko a nahiyar Afrika. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku