in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta amince da wani shirin gyara bangaren makamashi
2016-08-17 10:49:44 cri
Gwamnatin Benin ta rattaba hannu kan wani shirin gyara bangaren makamashi domin samarwa kasar makamashi cikin dogon lokaci, mai inganci kana cikin farashi mai rahusa, in ji wata sanarwa ta gwamnatin kasar da aka fitar a ranar Litinin a birnin Cotonou, hedkwatar tattalin arzikin Benin. Manyan batutuwa guda 28 dake kunshe da wannan shirin, dake tantance ayyukan da za a gudanar bisa ga tasirin da ake jira, an gano su bisa tushen ka'idoji da dama, musamman ma aiki tare da bangaren masu zaman kansu wajen zuba kudi kan wasu bangarori daban daban da kuma yin amfani da karfin makamashi a matsayin daya daga cikin hanyoyi mafi sauri kuma mafi kawo riba domin fuskantar matsalar gibin makamashi. A cikin watan Yulin da ya gabata, gwamnatin Benin ta dauki niyyar zare kimanin Sefa biliyan 30 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 50 daga cikin kudin kasafin kasa, domin karfafa karfin cikin gida na samar da makamashi a dukkan fadin kasar Benin ta yadda za a iya kawo karshen matsalar rashin wutar lantarki a cikin watan Oktoba mai zuwa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China