A cewar sanarwar, domin saukaka fitar da kayayyakin kasar Benin zuwa kasashen kungiyar ECOWAS, gwamnatin Benin ta sanar da wani kudurin da ya shafi shiryawa da tsarin tafiyar da yankin masana'antu a kasar Benin.
Bisa shiri na wannan kuduri ne ake amincewa masana'antu aiki da tsarin yankin masana'antu. Wasu masana'antun da aka amincewa na fuskantar matsalolin da dama na fitar da kayayyakinsu tun lokacin kafa dokokin farko da kuma lokacin fara aikin harajin waje na hadin gwiwa na kungiyar ECOWAS, a cewar sanarwar. A cewar wannan sanarwa, matsalolin da kamfanonin suke fuskanta na da nasaba da rashin ingancin tsarin yankin masana'antu da alfanun takardar farko ta gamayyar. Bisa rashin wannan takardar farko ta gamayyar, masana'antun da aka amincewa ba su iya fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen ECOWAS, har a Nijeriya, in ji sanarwar. Game da haka, in ji sanarwar, domin kawar da wannan matsala da kuma baiwa wadannan masana'antu damar cin gajiyar shige da fice cikin 'yanci na kayayyakinsu, an tsai da yiyuwar, ga masana'antun da aka amincewa na watsi da tsarin yankin masana'antu da kuma yin amfani da matakin zuba jari, idan haka ya zama wajibi. (Maman Ada)