Gasar al'adun na da manufar bunkasa al'adun kasar Benin baki daya, a fannin kide kide, raye raye, wasannin kwaikwayo, silima da zane zane, har ma da kokarin ingiza masu fasaha kara himmatuwa wajen bullo da fasahohi na kwarai da kuma karfafa saninsu a fannonin da suka fi mayar da hankali, in ji Ali Wassi Sissy, shugaban wannan gasar al'adu. Kyaututukan da za a bayar sun hada da kyautar fitaccen faifan zamani, kyautar fitaccen faifan gargajiya, kyautar fitaccen faifan zamani bisa tunanin al'adun gargajiya, kyautar fitaccen faifan Hip-hop, Rapp, Gospel, da kuma kyautar gwanin gabatar da wasannin kai tsaye. (Maman Ada)