in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gungun gwamnonin Afrika na bankin duniya da IMF zai yi taro nan gaba a Cotonou
2016-07-30 12:57:15 cri
Gungun gwamnonin Afrika na bankin duniya da asusun bada lamuni na IMF zai gudanar da wani taron shekara daga ranakun 4 zuwa 5 ga watan Augusta a Cotonou, hedkwatar tattalin arzikin Benin, in ji darektan fada a ma'aikatar kula da cigaba, mista Ruffino d'Almeida.

Bisa taken "Kara rubanya tallafin hukumomin Breton Woods domin amsa manya bukatu, karfafa cigaba da bunkasa sauye sauyen Afrika", taron zai baiwa mahalarta damar gudanar da musanyar kwarewa, ta hanyar wani taron karawa juna sani da kuma shirya kundin Gungun Afrika na shekarar 2016.

Gungun gwamnonin Afrika na bankin duniya da IMF, da aka fi sani da "Caucus Africain" nada makasudin karfafa hanyar gwamnonin nahiyar Afrika kan muhimman batutuwan dake da nasaba da cigaban tattalin arziki dana al'umma na shiyyar a cikin hukumomin Breton Woods. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China