A yayin bikin na bana, wasu jami'ai da 'yan kasuwa daga kasashen hanyar siliki, sun bayyana cewa, an cimma nasarar aiwatar da wasu shirye-shirye na cinikayya, ta hanyar gudanar da irin wannan bikin baje koli na kasa da kasa, lamarin da ya sa hakan ya zama wani muhimmin dandali na karfafa mu'amalar ciniki, da al'adu a tsakanin kasashen dake kan hanyar siliki.
Bikin baje kolin abincin halal, da kayayyakin musulunci da aka gudanar har sau goma, ya riga ya kasance daya daga cikin manyan bukukuwan baje kolin abincin halal guda takwas na kasa da kasa.
A daya bangaren kuma, yayin gudanar wannan taro, an gabatar da taron kolin hadin gwiwa da bunkasuwar kamfanonin kasashen dake cikin shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, inda mataimakin shugaban kungiyar inganta harkokin ciniki ta kasar Sin Zhang Wei, ya bayyana cewa, ba ga kasancewar shirin a matsayin hanya ta samar da dama mai kyau ga kasar Sin wajen ayyukan bude kofofin ta ga kasashen ketare, haka kuma, matakin zai ba da damar habaka hadin gwiwar kasashen da abin ya shafa, game da harkokin masana'antu da cinikayya a fannoni daban daban.
Kaza lika, bisa kididdigar da kungiyar ta yi, an ce, cikin shekarar 2015, adadin jarin kai tsaye da kasar Sin ta zuba ga kasashe 49 dake cikin shirin zirin tattalin arzikin siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni 21 ya kai dalar Amurka biliyan 14.82, adadin da ya karu da kashi 18.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2014. Kana ya kai kashi 12.6 bisa dari na jimillar jarin da kasar Sin ta zuba ga kasashen ketare. (Maryam)