Kungiyar bankunan kasar Sin ta sanar da cewa a yanzu haka ana iya amfani da katin kungiyar, a kasashe da yankuna kimanin 50 daga cikin 60 ko fiye, wadanda shirin "ziri daya da hanya daya" ya shafa. Lamarin da ke nuna cewa katin kungiyar bankunan Sin, ya zama muhimmin abu da ya hada kasar Sin da wadannan kasashe.
Wani babban jami'in kungiyar bankunan kasar ta Sin ya bayyana cewa, a matsayin kasa wadda ke cibiyar yankin tsakiyar Asiya, da kasashe 6 na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, kasar Kazakhstan na taka muhimmiyar rawa a kasuwar katunan bankunan.
Kungiyar bankunan Sin ta ba da gundummawa ga hadin gwiwar kasashen biyu a fannin hada-hadar kudi, ta hanyar hadin gwiwa tare da manyan hukumomin hada-hadar kudi na kasar Kazakhstan, wajen habaka yankunan da ake amfani da na'urorin ATM da POS, da gabatar da katin farko dake da kananan na'urar lantarki a kasar, da kara inganta katunan da ake amfani da su a kasar. (Lami)