A ranar Litinin ne aka kammala bikin baje kolin kayayyakin abincin Halal na kasa da kasa da aka shirya a lardin Qinghai da ke arewa maso yammacin kasar Sin.
Bikin na tsawon kwanaki hudu ya samu halartar sama da 'yan kasuwa 3,500 da kamfanoni 1,126 daga kasashe da yankuna 39 na duniya, inda aka baje kolin kayayyakin abinci kimanin 1,100.
Bugu da kari, a lokacin bikin na bana, an sanya hannu kan yarjejeniyoyin kayayyakin abincin Halal da suka kai dala miliyan 650, adadin da ya karu da kashi 16 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bara.
A yayin bikin na wannan karo, jakadun kasashe da wakilansu daga kasashen kudu maso gabashin Asiya da Gabas ta Tsakiya sun kira taron karawa juna sani don tattauna yadda masana'antun Halal ke samun ci gaba a kasashensu.
Bayanai na nuna cewa, akwai kimanin musulmai miliyan 1 a lardin Qinghai, ko kuma daya bisa biyar na yawan jama'ar lardin. Sannan akwai abinci musulmi da kayayyakin kamfanonin da ke samar da irin wadannan abinci sama da 1,000, da kuma ma'aikata da ke aiki a irin wadannan kamfanonin Halal 300,000.
An kuma yi kiyasin cewa, a shekarar da ta gabata, darajar kayayyakin abincin Halal a yankin ta kai Yuan biliyan 18. (Ibrahim)